Isa ga babban shafi

Zelensky ya nemi taimakon kasashen Larabawa don kawo karshen yakin Ukraine

Da yake jawabi a taron kasashen Larabawa da aka yi a Jeddah a ranar Juma'a, shugaba Volodymyr Zelensky ya bukaci kasashen Larabawa da su goyi bayan shirinsa na samar da zaman lafiya ta hanyar kawo karshen yakin Rasha a Ukraine.

Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy kenan lokacin da ya isa kasar Saudiyya.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy kenan lokacin da ya isa kasar Saudiyya. VIA REUTERS - SAUDI PRESS AGENCY
Talla

Shugaban kasar Ukraine Volodymyr Zelensky ya isa kasar Saudiyya domin halartar babban taron kungiyar kasashen Larabawa, a ziyarar sa ta farko zuwa yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan mamayar da Rasha ta yiwa kasarsa a watan Fabrairun 2022.

A cikin jawabinsa Zelensky ya ce: “Ba mu mallaki irin makami mai linzamin da abokan gaba suka mallaka ba, kuma ba mu da karfin sojin sama da ya kai karfin makiya, amma muna da karfi saboda mun san cewa muna da gaskiya.”

Guda daga cikin mahalarta taron, ya shaidawa AFP cewa, kasar Saudiyya ce ta gayyaci Zelensky ba wai kungiyar ba.

Haka zalika daga cikin shugabannin da suka halarci wannan taro, akwai shugaban Syria da kasarsa ta jima tana fuskantar tsangwama daga yankin, wato Bashar al-Assad.

Taron da ke gudana a Saudiyya na zuwa ne daidai lokacin da kasar ke kokarin gyara alakar diflomasiyyarta a yankin Gabas ta Tsakiya da sauran nahiyoyi.

Ganawar ta biyo bayan wani dogon zango na diflomasiyya mai cike da rudani sakamakon cimma yarjejeniyar da kasar China ta kulla da Iran da aka sanar a watan Maris.

Tun daga wannan lokacin ne Saudiyya ta maido da huldar da ke tsakaninta da kasar Siriya tare da kara kaimi wajen samar da zaman lafiya a kasar Yemen, inda take jagorantar kawancen soji kan 'yan tawayen Huthi masu samun goyon bayan Iran.

Sai dai ba kowace kasa bace a yankin ke kokarin gyara alaka da gwamnatin shugaba Assad.

A farko wannan watan ne, Qatar ta ce ba za ta daidaita dangantakar da ke tsakaninta da gwamnatin Assad ba, amma ta lura cewa hakan ba zai zama wani cikas ba ga hadin kan kungiyar kasashen Larabawan.

Saudiyya dai ta taka rawa wajen kwashe fararen hula daga Sudan a lokacin da fada ya barke a watan Afrilu, kuma a halin yanzu tana karbar bakuncin wakilan bangarorin da ke rikici da juna a Sudan a wani yunkuri na kawo karshen tsagaita bude wuta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.