Isa ga babban shafi

Dubban mutane ne suka halarci bikin tunawa da kisan kiyashin Srebrenica

Dubban mutane daga sassan kasar Bosnia da kuma ketare ne suka hallara a birnin Srebrenica a ranar Talata, domin gudanar da bikin tunawa da kisan kiyashin da aka yi a yankin gabashin kasar a shekarar 1995, da kuma yin jana'izar mutanen da aka tono wani bangare na sassan jikinsu daga manyan kaburburan da aka gano ta hanyar amfani da gwajin kwayoyin halitta na DNA.

Mejra Djogaz, mai shekaru 71 kusa da kabarin mijinta mai suna Omer, da aka kashe a wancan lokaci.
Mejra Djogaz, mai shekaru 71 kusa da kabarin mijinta mai suna Omer, da aka kashe a wancan lokaci. AFP
Talla

Shekaru 28 bayan kisan gilla mafi muni da aka yi a yankin Turai wanda aka ayyana fiye da kisan kare dangin da aka yiwa Yahudawa wanda ake kira da Holocaust, za a yi jana'izar maza 27 da yara maza uku a ranar Talata a wata babbar makabarta da aka binne sassan jikin mutane fiye da 6,600 wadanda aka gano gawawwakinsu a wancan lokaci.

Kisan kiyashin Srebrenica shi ne mafi muni a yakin Bosnia na 1992-95, wanda ya zo bayan wargajewar Yugoslavia abin da ya haifar da yakin basasa mafi muni wanda ya sanya Sabiyawan Bosnia adawa da sauran manyan kabilun Croats da Bosniaks guda biyu.

Babbar makabartar da aka binne sassan jikin mutane fiye da 6,600 a Srebrenica.
Babbar makabartar da aka binne sassan jikin mutane fiye da 6,600 a Srebrenica. REUTERS/Dado Ruvic

A ranar 11 ga watan Yuli 1995, Sabiyawan Bosnia suka mamaye wata mafakar tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya a Srebrenica, inda suka raba akalla musulmi 8,000 bayan da suka fatattake su zuwa cikin dazuzzuka a kusa da wannan gari, tare da binsu suna musu yankan rago.

Wadanda suka aikata wannan aika-aika sun yi ta boye gawarwakin wadanda aka kashe a cikin kaburbura da aka tona, domin boye shaidar laifukan yaki da suka aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.