Isa ga babban shafi

China ta yi barazanar daukar tsauraran matakai kan Taiwan

Kasar China ta lashi takobin daukar tsauraran matakai kan Taiwan, kuma wannan ya biyo bayan ziyarar da mataimakin shugaban kasar Taiwan din William Lai ya kai kasar Amurka a karshen mako da ta ce tana sa ido sosai.

Shigaban China Xi Jinping kenan.
Shigaban China Xi Jinping kenan. AP - Mark Schiefelbein
Talla

Lai wanda ke kan gaba a zaben shugaban kasar Taiwan a shekara mai zuwa ya yada zango ne a Amurka yayin da yake kan hanyarsa ta shiga Paraguay, domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar Santiago Pena.

Kasar China dai na ci gaba da ikirarin tsibirin na Taiwan mallakarta ne, tare da cewar ko ba jima zai dawo karkashin ikonta.

Gabanin tafiyar Lai, China ta rubanya kutsen da sojojinta ke a cikin ruwa da sararin samaniyar yankin Taiwan idan aka kwatanta da shekarar bara.

A ranar Laraba, ma'aikatar tsaron kasar ta ce an gano jiragen yakin kasar China 33 da jiragen ruwa 6 a kusa da tsibirin a cikin tagar sa'o'i 24 kadai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.