An mayar da mutane 776 kasar Iraqi daga sansanin Al-Hol a Syria
Rahotanni daga kasar Syria na bayyana komawa kasar Iraqi na mutane 776 da suka kasance iyalai 192 da suka bar sansanin Al-Hol na kasar Syria.Wadanan mutane sun kasance 'yan uwan mayakan kungiyar IS.
Wallafawa ranar:
A jiya Asabar ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta Syrian Observatory for Human Rights (OSDH) ta tabbatar da kwashe wadanan mutane a cikin motocin bas daga sansanin na Al-Hol da ke arewa maso gabashin Syria zuwa Iraqi.
Akalla mutane kusan 50,000 ne ke zaune a sansanin Al-Hol dake karkashin gwamnatin Kurdawa ya ke dauke da tarin jama’a ganin ta yada ake fama da cunkoso.Wasu alkaluma na dada bayyana cewa,wurin na kumshe da 'yan gudun hijirar Syria ne, 'yan gudun hijirar Iraqi da kuma baki fiye da 10,000 daga kasashe kusan sittin, iyalan mayakan kungiyar ta IS.
Da isar wadanan mutane a kasar Iraqi, hukumomin kasar sun bayyana cewa za a tsare su na tsawon makonni har ma da watanni da dama a sansanin Al-Jadaa, kafin su iya komawa yankunansu na asali.
Sai dai komawar mutane Iraqi na ci gaba da haifar da cece-kuce a tsakanin wani bangare na al'umma da tsawon shekaru uku suka fuskanci hare-hare dag ayan kungiyar IS ,da kuma cin zarafi daga mayakan kungiyar IS, wacce ta mamaye kusan kashi uku na kasar Iraqi daga shekara ta 2014 zuwa 2017.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu