Isa ga babban shafi

Biden da XI sun amince su koma tuntubar juna kan tsaro

 A lokacin ganawarsu ta keke da keke da suka yi da juna cikin shekara guda a  jiya laraba, Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na China Xi Jinping, sun amince su sake bude layukan wayoyin  tuntuba na fadar shugaabancin kasshensu , domin sake maido da tattaunawa tsakanin sojoji, tare da yin aiki wajen rage sarrafa kwayar Fentanyl, wanda ya nuna cewa ana samun ci gaba mai yawa ta wannan fanni.

Shuwagabanin kasashen China da Amurka na tattaunawar dinke baraka a San Farancisico a ranar 15-11-2023
Shuwagabanin kasashen China da Amurka na tattaunawar dinke baraka a San Farancisico a ranar 15-11-2023 AP - Doug Mills
Talla

Biden da Xi sun yi ganawar tasu ta tsawon mintina 15 ne a wani wajen dake wajen birnin San Farancisco na kasar Amurka inda suka tattauna kan fannonin da ke haifar da tsaurin dangantaka tsaknin Amurka da China.

Shuwagabanin biyu, sun bukaci maido da tsarin  tuntubar junan da suke yi ta wayar telefon a  tsakaninsu,  bayan da  China ta dakatar ita, domin nuna takaicinta kan ziyarar da shugabanr majalisar wakilan Amurka, uwargida Nancy Pelosi ta kai yankin Taiwan cikin watan ogustan bara. Biden ya ce,  sun sake komawa tattaunawar kai tsaye, haka kuma ta   gaskiya a tsakaninsu

Har ila yau shugaban Amurka Joe Biden ya ce, Shugaba Xi ya amince da ci gaba da tattaunawa tsakanin manyan jami’an kasashensu, dukkaninsu kuma sun amince, su koma wa tattaunawar telefon din da suke yi, Wanda zai basu damar magance banbance-banbancen dake tsakaninsu cikin gaggawa.

To’ sai dai, a cikin wani jawabin dake bakanta wa kasar China, Biden ya sanar da manema labarai cewa, shi ba zai canza ra’ayinsa da ya danganta shugaban China Xi a matsayin dan kama karya.

Biden ya kara da cewa, tabas shugaba Xi dan kama karya ne da ke jagorancin wata kasa, da ke  bin tafarkin Kominisanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.