Isa ga babban shafi

Shugaba Vladimir Putin ba zai halarci taron kasashen G 20

Shugaban Rasha Vladimir Putin ba zai halarci taron kasashen G 20 da kasar India ke karbar bakucin ba. Vladmir Putin  zai halarci taron ta hanyar bidiyo a taron koli na rukunin Ashirin da aka shirya yi a ranar Laraba,sanarwa daga gidan talabijin na kasar Rasha a yau Lahadi. 

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin. 路透社。
Talla

A sanarawr gidan talabijen na kasar ta Rasha ba a  fayyace ta wane tsari ne shugaban na Rasha zai shiga taron ba, shekara ta biyu a jere, Shugaban na Rasha Vladimir Putin bai amsa gayyatar da aka yi masa na wakilcin Rasha a zahiri a taron G20 ba, yayin da aka ware shugaban daga fagen kasa da kasa saboda harin da ya kaiwa Ukraine a watan Fabrairun 2022. 

Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan
Shugaban Rasha Vladmir Putin kenan via REUTERS - SPUTNIK

Wani abin lura   shine tun bayan barkewar cuta ta Covid-19, har ma tun lokacin da aka fara rikici a Ukraine, Vladimir Putin ba kasafai yake yin balaguro zuwa kasashen waje ba, kamar yadda ya yi a China a watan Oktoba, inda ya tattauna da Shugaban na China Xi Jinping. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.