Isa ga babban shafi

Safarar mutane: Indiya na binciken yadda wasu 'yan kasarta suka fada wani jirgi da Faransa ta tsare

Kasar Indiya ta kaddamar da bincike kan yadda wasu Indiyawa 303 suka kasance a wani jirgin hayar da aka dakatar a Faransa a makon da ya gabata saboda zargin safarar mutane, kamar yadda hukumomin jihar Gujarat da ke yammacin Indiya suka bayyana.

Wani fasinja da ya taso daga Nicaragua kenan cikin jirgin samfurin A340, wanda hukumomin Faransa suka tsare sakamakon zargin safarar kananan yara.
Wani fasinja da ya taso daga Nicaragua kenan cikin jirgin samfurin A340, wanda hukumomin Faransa suka tsare sakamakon zargin safarar kananan yara. REUTERS - FRANCIS MASCARENHAS
Talla

A ranar Juma’a ne, hukumomin Faransa suka hana jirgin tashi zuwa Nicaragua.

Jirgin dai rahotanni sun ce ya taso ne daga Hadaddiyar Daular Larabawa dauke da kananan yara 11 da babu wanda ke tare da su a cikin fasinjojin, kuma 276 daga cikinsu sun koma gida Indiya a ranar Talata.

Sanjay Kharat, wani babban jami’in ‘yan sanda na Gujarat, ya ce hukumomi sun samu sunaye da adireshi na mutane 21 daga jihar da ke cikin jirgin, kuma masu bincike na kokarin tantance wadanda suka dauki nauyin jigilar yaran.

Kamfanin jiragen saman Legend na Romania ne ke tafiyar da harkokin zirga-zirgar wannan jirgi.

A cewar rahotanni, lauyan kamfanin mai suna Liliana Bakayoko ta ki bayyana sunan wanda ya yi hayar jirgin, saboda yarjejeniyar sirri ta kwangila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.