Isa ga babban shafi

An kashe sama da Dala tiriliyan biyu a bara wajen samar da tsaro a duniya-Rahoto

Kudin da kasashen duniya ke kashewa wajen samar da tsaro ya karu da kashi 9 cikin 100, inda ya kai dala tiriliyan 2.2 a bara kamar yadda wata cibiyar bincike kan ayyukan soji ta Birtaniya ta bayyana.

Kudin da kasashen duniya ke kashewa wajen samar da tsaro ya karu da kashi 9 cikin 100.
Kudin da kasashen duniya ke kashewa wajen samar da tsaro ya karu da kashi 9 cikin 100. REUTERS/Maxim Shemetov
Talla

Ana sa ran adadin kudin ya kara karuwa a wannan shekara ta 2024 saboda yakin da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma rikicin da ake fama da shi a Ukraine, baya ga zaman tankiyar da ke zafafa a yankin tekun India da Pacific.

Kazalika sabon rahoton da Cibiyar Nazirin Ayyukan Soji ta Kasa da Kasa mai cibiya a birnin London  ta wallafa ya kuma ambaci barazanar da ke tsananta a yankin tekun Arctic da kuma yadda Koriya ta Arewa ke gina makaman nukiliya.

Har ila yau rahoton ya nuna damuwa kan China da kuma yadda sojoji ke juyin mulki a kasashen Sahel, abubuwan da suka ce suna bada gudunmawa wajen haddasa rashin tsaro a duniya.

Rahoton ya ce, matakin Iran na bai wa mayakan Houthi makamai a Yemen da kuma jirage marasa matuka ga Rasha ya nuna yadda Tehran ke samun karfin fada-a-ji a yankin mai fama da rikici.

Wani bangare na sakamakon da rahoton ya tattaro, ya nuna cewa, Rasha ta yi asarar manyan tankokin yaki 3,000 a lokacin fafata yakinta da Ukraine kuma tuni kasashen duniya suka dauki darasi daga yakin na Ukraine, abin da ya sa suke tanadin makamai a yanzu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.