Isa ga babban shafi

Majalisar Dattijan Birtaniya ta yi watsi da shirin jibge bakin haure a Rwanda

Majalisar dattijan Birtaniya ta yi watsi da shirin Firaminista Rishi Sunak game da aikin girke ‘yan gudun hijira da masu neman mafakar da ke shigowa kasar a Rwanda shirin da tun a farko ya gamu da kakkausar suka daga kungiyoyin kare hakkin dan adam.

Zauren Majalisar Birtaniya.
Zauren Majalisar Birtaniya. © Andy Bailey / AP
Talla

Birtaniya na shirin mayar da Rwanda sansanin jibge bakin hauren da ke shiga kasar ta Turai duk kuwa da yadda kotun kolin kasar ta ki amincewa da batun bayan da ta bayyana Kigali a matsayin kasar da bata da cikakken tsaro.

A zaman majalisar dattawan ta Birtaniya jiya Litinin ne ya bukaci gwamnatin kasar ta yi biyayya ga dokokin cikin gida da kuma na kasa da kasa wajen tabbatar da tsaron bakin hauren da ke neman mafaka a kasar.

Yayin zaman majalisar ‘yan majalisu 277 sun bukaci gudanar da bincike don tabbatar da tsaron Rwanda gabanin amincewa da shirin girke bakin hauren yayinda 167 suka nemi ayi watsi da batun baki daya.

A watan Janairun da ya gabata ne ‘yan majalisar wakilan Birtaniya suka sahale dokar girke bakin hauren mai cike da tarnaki gabanin majalisar dattawan da dakatar da tattaunawa kan kudirin.

Tuni dai Birtaniya ta damkawa Rwanda dala miliyan 300 don fara aikin ginin sansanonin da za a rika jibge bakin hauren.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.