Isa ga babban shafi

Al'amura sun farfado yadda ya kamata bayan kawo karshen cutar Covid 19 - MDD

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rayuwar al’ummar duniya ta koma yadda ta ke a fannin ci gaba gabanin bullar annobar Covid-19, sai dai ta yi gargadi kan yadda aka samu wagegen gibi a tsakanin kasashe masu hannu da shuni da matalauta wajen farfadowar tattalin arziki.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce rayuwar al’ummar duniya ta koma yadda ta ke a fannin ci gaba gabanin bullar annobar Covid-19.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce rayuwar al’ummar duniya ta koma yadda ta ke a fannin ci gaba gabanin bullar annobar Covid-19. AFP - MEHDI FEDOUACH
Talla

Rahoton da Hukumar Bunkasa kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya  ta fitar a Larabar nan, ya ce wannan farfadowar da aka samu ta biyo bayan ci baya na shekaru 2 da aka samu, lokacin da a shekarar 2021 da 2022, mizanin auna ci gaban rayuwar al’umma ya samu nakasu har sau biyu a karon farko tun da aka bijiro da shi shekaru 35 da suka wuce, sakamakon bullar annobar Covid-19, wadda ta haddasa koma -baya a ci gaban da aka samu na shekaru 5.

Yanzu Hukumar Bunkasa Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta yi hasasshen samun ci gaba mai dimbim yawa a nan gaba, kamar yadda rahoton ya nuna.

Hasashen na shekarar 2023 ya nuna ci gaba a dukkan fannoni da suka hada da batun tsawon rayuwa, ingantuwar ilimi da halin rayuwa, sai dai tasirin annobar Covid-19 da yakin da ake a Ukraine ya dan haddasa nakasu a hasashen.

Rahoton ya nuna Switzerland da Norway da kuma Iceland a matsayi na kololuwa a mizanin auna ci gaban rayuwa da sauran manyan kasashe masu kumban susa, a yayin da Somalia da Sudan ta Kudu da Jamhuriyar Tsakiyar Afrika sun tsinci kansu a kasan wannan mizani.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.