Isa ga babban shafi
Nijar-Faransa

Macron ya ziyarci kaburruran sojojin Nijar da aka kashe

Bayan ziyarar kwanaki biyu a Cote d’Ivoire, shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya yada zango a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar a marecen Lahadi, inda ya jajanta wa al’ummar kasar dangane da mutuwar sojoji 71 a harin da ‘yan ta’adda suka kai a garin Inates. Macron da takwaransa na Nijar, Muhammadou Issofou sun ziyarci kaburruran sojojin.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Nijar, Muhammadou Issoufou
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwaransa na Nijar, Muhammadou Issoufou Ludovic MARIN / POOL / AFP
Talla

Shugabannin biyu sun ce za su gana cikin watan gobe a Faransa, don sake daura damarar fada da ayyukan ta’addanci a Sahel.

Kuna iya latsa alamar sautin da ke kasa domin sauraren cikakken rahoton Souley Maje Rejeto.

01:33

Macron ya ziyarci kaburruran sojojin Nijar da aka kashe

Ziyarar Macron na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin al'ummar Nijar bukaci Faransa da ta gaggauta janye dakarunta na Barkhane saboda rashin tasirinsu a kasar a cewarsu, ganin yadda suka gaza dakile hare-hare da dama ciki har da wanda ya hallaka sojin na Nijar a barikin Inates.

Sai dai shugaba Macron ya jaddada cewa, sojojin na Faransa za su ci gaba da zama domin kuwa gwamnatin Nijar ce ta bukaci a girke su domin fada da ayyukan ta'addanci.

Tuni Macron ya koma gida bayan kammala ziyarsa a kasashen na Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.