Isa ga babban shafi

Al'ummar Jamhuriyar Nijar sun yi bikin Sallah Karama

Yau al’ummar Jamhuriyar Nijar suka gudanar da Sallah Karama bayan sanar da ganin jinjirin watan Shawwal da mahukuntan kasar suka yi a jiya Litinin.

Al'ummar Musulmi yayin Salla, a babban Masallacin Juma'a na birnin Agadez dake Jamhuriyar Nijar. (Hoto domin misali)
Al'ummar Musulmi yayin Salla, a babban Masallacin Juma'a na birnin Agadez dake Jamhuriyar Nijar. (Hoto domin misali) MAPS/ Alessandro Penso
Talla

Bayanai sun ce mahukuntan na Nijar sun tabbatar da ganin jinjirin watan na Shawwal ne a jihohi akalla biyar da ke fadin kasar, abinda ya sanya suka bayyana wannan Talata 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar Sallah wadda tayi daidai da 1 ga watan Shawwal shekara ta 1445.

A yayin da Nijar ke bikin kammala Azumin watan Ramadana, akasarin kasashen Musulmi sun bayyana Laraba ne a matsayin ranar Sallar karama saboda rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin.

Daga cikin kasashen da suka cika kwanaki 30 a watan na Ramadana akwai Saudiya, Yemen, Syria, Masar, Iraqi, Hadaddiyar Daular Larabawa, da Lebanon, da Yankin Falasdinu da kuma Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.