Isa ga babban shafi
Faransa

Nicolas Sarkozy ya bayyana aniyar shi ta takarar shugabancin Faransa

Shgaban Fararnsa Nicolas Sarkozy ya kadamar da yakin neman zaben shi. wannan sanarwar na zuwa ne kasa da makonni 10 kafin ranar zaben shugaban kasar, duk kuwa da cewa har yanzu Mr Sarkozy yana bayan babbab abokin adawar shi na jama’iyyat Socialist Francois Hallade. Cikin wata hira da ya yi da gidan talibijin na TFI, Mr Sarkozy yace “Eh, ba shakka zanyi takara”, ya kara da cewa ya dauki wannan matakin ne saboda matsalolin da suke damun Faransa, Turai da ma duniya baki daya.Sarkozy ya kwatanta kanshi da dreban jirgin ruwa, da ke tsakiyar tuku, a daidai lokacin da iska mai karfin gaske, ke barazanar yi awon gaba da jirgin.Ya ce yana abin da zai fada wa Faransawa, kuma yana da bukatar da yake son mika musu.Shugaban ya dade yana hirarrraki ta tsahar talibijin, amma sai a wannan ranar laraban ya shaida wa ‘yan kasar fatan shi na tsayawa don yi takarar shugaban ci kasar. 

Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy.
Shuagaban Faransa Nicolas Sarkozy. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.