Isa ga babban shafi
Norway

Kotu ta yankewa Breivik hukuncin daurin shekaru 21

Wata kotu a birnin Oslo babban birnin kasar Norway ta yanke wa Anders Behring Breivik hukuncin daurin shekaru 21 a gidan yari bayan kama shi da laifin aikata ta’addanci wanda ya bindige mutane 77 a shekarar 2011.

Anders Behring Breivik Dan bindigar da ya kashe mutane 77 a kasar Norway
Anders Behring Breivik Dan bindigar da ya kashe mutane 77 a kasar Norway REUTERS/Heiko Junge/NTB Scanpix/Pool
Talla

Alkalai masu shari’a Biyar a kotun sun gano Brievik yana da hankalinsa bayan wasu sun yi zargin yana da tabin hankali. Wannan ne kuma ya kawo karshen makwanni 10 ana tabka shari’arsa.

A ranar 22 ga watan Yuli ne Brievik ya bindige mutane Takwas a Oslo sannan kuma ya sake bindige wasu mutane 69 yawancinsu matasa a wani tsibiri.

Karkashin dokar kasar Norway babu hukuncin daurin Rai da Rai ko hukuncin kisa, kololuwar hukunci shi ne daurin shekaru 21 a gidan yari. Sai dai ‘Yan Hursuna da ake tunanin za su zama barazana ga rayuwar Al’umma za’a iya ci gaba da tsare su a gidan yari har zuwa wani lokaci.

Brievik mai shekaru 33 ya amsa laifin shi wanda yace shi makiyin mabiya addinin Islama ne a Turai.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.