Isa ga babban shafi
Faransa

Jam’iyyar Sarkozy ta shiga rudanin Siyasa a Faransa

Jam’iyyar Tsohon Shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ta UMP ta fada cikin rudanin Siyasa bayan masu takarar neman shugabancin Jam’iyyar guda biyu sun yi ikirarin lashe zaben wanda dukkaninsu suka yi zargin an tabka magudi.

François Fillon tare da Jean-François Copé,da ke takarar shugabancin Jam'iyyar UMP a Faransa bayan sun kammala muhawara da juna.
François Fillon tare da Jean-François Copé,da ke takarar shugabancin Jam'iyyar UMP a Faransa bayan sun kammala muhawara da juna. REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Tsohon Sakatare Janar na Jam’iyar, Jean Francois Cope, da tsohon Firaminista, Francois Fillon su ne ke takara da juna kuma dukkaninsu sun ayyana samun nasara a zaben.

Wakilan Mista Cope sun yi ikirarin dan takararsu ya samu kuri’u 1,000 fiye da abokin takarar shi a zaben da Mambobin Jam’iyyar 300,000 suka kada kuri’a. A daya bangaren kuma Mista Fillon yace ya samu rinjayen kuri’u 223 tsakanin shi da Cope.

Ya zuwa yanzu dai hukumar zabe ba tace komi ba dangane da sakamakon zaben.

Dukkanin wakilan ‘Yan takarar guda biyu sun yi zargin samun kura kurai a zaben kuma har yanzu babu wani tabbacin lokacin da hukumar zabe za ta diba koken ‘Yan takarar don bayyana sakamakon zaben.

Duk dai wanda aka bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben shi ne zai jagoranci Adawa da gwamnatin Hollande na Jam’iyyar Gurguzu wanda ya kada Sarkozy a zaben shugaban kasa.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.