‘Yan kishin Rasha suna nan kan bakarsu
‘Yan tsagera a kasar Ukraine sun bayyana aniyarsu na ci gaba da shirin gudanar da zaben raba gardama domin neman ‘yancin kai a gabacin kasar, suna masu yin watsi da kiran shugaban kasar Rasha Vladimir Putin akan su dage gudanar da zaben.
Wallafawa ranar:
A ranar Lahadi ne ‘Yan tawayen suka shirya gudanar da zaben raba gardama domin kafa kasar Jamhuriyyar Donetsk.
Akwai fargabar yiyuwar ballewar rikici a Ukraine a yayin da Rasha da kasashen Tsohuwar daular Soviet ke bikin samun galaba akan Dakarun Jamus a yakin duniya na biyu.
Ana sa ran Shugaban Rasha Putin zai kai ziyara yankin Crimea da ya balle daga Ukraine a watan Maris a daidai lokacin da dakarun Rasha suka gudanar da atisaye a kan iyaka da Ukraine.
Kasashen Amurka da Turai sun yi barazanar sake kakabawa Rasha takunkumi idan har masu ra’ayinta a Ukraine suka jefa kuri’ar amincewa su balle daga Ukraine.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu