Isa ga babban shafi
Faransa

Kungiyoyin kwadago a Faransa sun bijirewa Gwamnati

Dubban mutane ne ake sa ran yau su gudanar da zanga zanga a kasar Faransa dan nuna rashin amincewar su da shirin gwamnatin kasar na sauya dokar ayyukan kasuwanci.Zanga zangar na zuwa a dai dai wani lokacin da baki ke cigaba da kwarara kasar dan halartar gasar cin kofin nahiyar Turai . 

Tutar kungiyar kwadagon Faransa CGT.
Tutar kungiyar kwadagon Faransa CGT. REUTERS/Stephane Mahe
Talla

Gwamnatin kasar na fatar ganin an kawo karshen zanga zangar inda take cewar ma’aikatan sun gaji, amma Sakatare Janar na kungiyar kwadago Phillipe Martinez yace an yanzu suka fara.

Kafin fara gasar kungiyoyin kwadago sun yi ta zanga zanga dan nuna bacin ran su da yadda gwamnatin kasar tayi gaban kanta wajen sauya dokar kwadago.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.