Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnati ta amince a yi zanga-zanga a Paris

Gwamnatin Faransa ta amince ma’aikatan kwadagon kasar su gudanar da zanga-zangar lumana a gobe Alhamis bayan da farko an haramta zanga-zangar ta adawa da sabuwar dokar kwadago.

Masu Zanga-zanga na arangama da jami'an tsaro a Faransa
Masu Zanga-zanga na arangama da jami'an tsaro a Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Shugaban kungiyar kwadago ta CGT Philippe Martinez, shi ne ya sanar da hakan, bayan wata ganawa da aka yi a yau laraba tsakanin wakilan gwamnati, da na kungiyar kwadagon da kuma kungiyar daliban kasar a birnin Paris.

Ya bayyana hakan a matsayin wata babbar nasara ga kungiyoyin kwadagon da kuma dimokuradiyya, a daidai lokacin da suke ci gaba da nuna rashin amincewa da wannan sabuwar doka.

Da farko dai gwmanatin kasar ta bayyana dalilai na tsaro domin hana shirya wannan zanga-zanga a gobe Alhamis, lamarin da ya haddasa kakkausar suka daga ‘yan siyasar kasar.

Wannan dai zai kasance karo na goma da ma’aikatan kwadago da kuma dalibai za su fito kan tituna domin yin zanga-zanga daga lokacin da aka kaddamar da sabuwar dokar, to sai dai sau da dama ana yin arangama tsakanin masu tarzomar da kuma jami’an tsaro a birnin Paris da sauran birane da ke yammacin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.