Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa ta bude cibiyar yaki da ta'addanci

A karon farko, gwamnatin Faransa ta bude cibiyar sauya tunanin matasa da ake zargi da daukan akidar mayakan jihadi.

Firaministan Faransa Manuel Valls
Firaministan Faransa Manuel Valls REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

Wannan dai na cikin matakan da gwamnatin kasar ke dauka don magance tsauraran akidu tsakanin matasa, ganin yadda ake kai ma ta hare-haren ta’addanci lokaci-lokaci

Cibiyar wadda aka kafa ta a wani babban gidan kasaita a tsakiyar Faransa mai suna Chateau de Pontourny, za ta fara karban mutane 25 masu shekaru 18 zuwa 30 daga cikin wata mai zuwa.

Kazalika, shirin wanda zai lakume Euro miliyan 40, zai bude wasu cibiyoyin a yankuna 12 na kasar don sauya tunanin matasan.

Matasan dai za su rika sanya rigar bai daya, sannan kuma za a rika kula da lafiayrsu tare da horar da su a fannonin da suka shafi tarihi da addini da falsafa da kuma kafafen yada labarai.

Firaministan kasar Manuel Valls ya bayyana cewa, yaki da ta’addaci a cikin gida, shi ne kalubale mafi girma da kasar ta fuskanta tun bayan yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.