Isa ga babban shafi
Columbia

Tattaunawa tsakanin 'yan tawayen FARC da Colombia ta samu koma baya

Al’ummar Kasar Colombia sun ki amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da Gwamnatin kasar ta kulla da ‘yan tawayen FARC domin kawo karshen yakin basasar da aka kwashe shekaru 52 ana fafatawa a kasar.

Wasu 'yan Colombia da basa goyon bayan afuwar da za'a yiwa 'yan tawayen FARC
Wasu 'yan Colombia da basa goyon bayan afuwar da za'a yiwa 'yan tawayen FARC © Reuters
Talla

Zaben raba gardamar da aka gudanar ya nuna cewa ‘yan kasar wadanda basu amince da yarjejeniyar ba sun samu sama da kashi 50% yayin da masu goyan bayan shirin suka samu sama da kashi 49% wato da kuri’u 54,000 suka samu nasara.

Masu sa ido a siyasar kasar sun ce, wadanda suka ki amincewa da shirin a karkashin tsohon shugaban kasa Alvaro Uribe na nuna rashin amincewar su da ahuwar bai daya da za’a yiwa Yan Tawayen da suka dade suna kashe mutane.

Shugaba Juan Manuel Santos ya amsa shan kaye a jawabin da ya yiwa al’ummar kasar, sai dai yace ba zai bada kai bori ya h au ba, zai ci gaba da neman hanyar zaman lafiya da yan tawayen har sai wa’adin mulkin sa ya kare.

Shima shugaban ‘yan tawayen Rodrigo Timochenko Jimenez ya tabbatar da matsayin su na ci gaba da tattaunawar.

Ana saran bangarorin biyu su koma tattaunawa a kasar Cuba dan sake fasalin yarjejeniyar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.