Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa na kwashe 'yan gudun hijirar Calais

Gwamnatin Faransa ta girke jami’an tsaro kimanin dubu 1 don kula da aikin kwashe ‘yan gudun hijira da ke samun mafaka a sansanin Calais.

Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Calais na Faransa
Wasu daga cikin 'yan gudun hijirar Calais na Faransa Reuters/Pascal Rossignol
Talla

Kimanin ‘yan gudun hijira dubu 7 ne ke zaune cikin mawuyacin hali a sansanin bayan akasarinsu sun kaurace wa tashe-tashen hankula daga kasashensu na asali da suka hada da Syria.

‘Yan gudun hijirar sun yi layi don tantance su kafin shiga motocin da aka tanada da za su kwashe su daga sansanin zuwa wasu wuraren zama na daban a Faransa.

To sai dai ana fargaban cewa, akwai wasu ‘yan gudun hijirar da za su bijirewa don ganin ba a kwashe su ba saboda muradinsu na tsallakawa Birtaniya.

Hukumomin kasar sun yi hasashen kwashe mutane dubu 2 da 500 a yau Litinin don rarrabasu a wurare 450 da gwamnatin ta tanadar wa bakin.

A gobe Talata ne, ake sa ran rushe sansanin baki daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.