Isa ga babban shafi
Faransa

Faransa: Le Pen ta kaddamar da yakin neman zabenta

Shugabar jam’iyyar adawa FN ta ‘Yan kishin kasa a Faransa Marine Le Pen ta kaddamar da yakin neman zabenta a yau Asabar a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 23 ga watan Afrilu.

'Yar takarar Jam'iyyar FN Marine Le Pen a Faransa
'Yar takarar Jam'iyyar FN Marine Le Pen a Faransa REUTERS/Jacky Naegelen
Talla

Le pen ta wallafa jerin manufofinta 144 ga Faransawa, da suka hada da ficewar kasar daga kungiyar kasashen Turai masu amfani da kudin euro da kara kudaden haraji ga ma’aikatan kwadago baki da suka shigo Faransa.

Le Pen dai na adawa da kudin bai-daya na euro da Kungiyar Tarayyar Turai ke amfani da shi.

A cikin manufofin da ta wallafa a shafinta na Intanet ta ce idan har sauran mabobin kasashen Turai suka ki amincewa da bukatunta to za ta gudanar da zaben raba gardama domin tantance makomar Faransa a kungiyar.

A gobe ne dai Le pen za ta gabatar da wani babban jawabi game da takararta a Lyon.

Hasashe a game da zaben Faransa ya nuna Le Pen za ta samu nasara a zagaye na farko amma za a doke ta a zagaye na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.