Isa ga babban shafi
Faransa-Amurka

Anne Hidalgo ta kare birnin Paris

Magajiyar birnin Paris uwargida Anne Hidalgo ta kare birnin daga kalaman da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya furta, inda ya danganta Paris zama sansanin yan ta’ada.

Anne Hidalgo Magajiyar birnin  Paris
Anne Hidalgo Magajiyar birnin Paris © REUTERS/Benoit Tessier
Talla

A lokacin ziyarar da take yi a Tokyo kasar Japon domin tallata birnin na Paris Japon.
Hidalgo ta ce Paris kalau yake, baya da wata damuwa balantana a danganta shi da sansanin yan ta’ada
A kokarinsa na kare manufar siysarsa kan baki, ne, a ranar juma’ar da ta gabata shugaba Donald Trump ya ce ya bukaci wani abokinsa da kar ya je Paris saboda hadarin da birnin keda shi

A lokacin da take mayar masa da martani uwargida Hidalgo tace babu wanda ya taba nuna yatsa kan yadda ake sayar da makamai a shagunan manyan birnanen kasar Amurka, wadanda kuma ake aikata duk wata irin ta’asa da su, al’amarin da tace ba yadda abokin hadi ko kadan.

Magajiyar birnin na Paris ta kara da cewa birnin Paris kalau yake, yana kuma kamar ko wane birni na Duniya, domin kuwa a halin da Duniya ke ciki yanzu babu wani babban birni na duniya da baya fuskantar barazanar ta’addanci.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande a ranar asabar da ta gabata ya mayarwa Donald Trump martani, da ya daina danganta kasar ta Faransa sansanin yan ta'ada.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.