Isa ga babban shafi
spain

Yankin Catalonia na bikin ranar 'yanci a yau

Akalla mutane miliyan biyu ne suka yi fitar dango, a birnin Barcelona yau Litinin, domin bikin zagayowar ranar ‘yancin yankin Catalonia, wadda suka yiwa lakabi da ‘Diada’. Babbar manufar taron miliyoyin jama’ar a yau dai shi ne, nuna goyon bayansu ga bukatar ballewar yankin na Catalonia daga kasar ta Spain.

A duk ranar 11 ga kowane watan Satumba ne, al’ummar yankin Catalonina ke gudanar da Bikin Diada ko kuma ranar ‘yanci’ domin tunawa da ranar da Sarkin Spain Boourbon Philip ya kwace iko da birnin Barcelona.
A duk ranar 11 ga kowane watan Satumba ne, al’ummar yankin Catalonina ke gudanar da Bikin Diada ko kuma ranar ‘yanci’ domin tunawa da ranar da Sarkin Spain Boourbon Philip ya kwace iko da birnin Barcelona. Reuters
Talla

Ana gudanar da wannan biki ne yayinda ake zaman dar-dar, bisa shirin gwamnatin yankin na Catalonia kan kada kuri’ar raba gardama dangane da bukatar ballewar yankin daga Spain.

Duk kuwa da cewa babbar kotun kasar ta bada umarnin dakatar da kada kuri’ar raba gardamar, wadda aka shirya gudanarwa a ranar 1 ga watan Oktoba mai zuwa, har zuwa lokacin da kotun ta yanke hukuncin karshe kan batun.

A duk ranar 11 ga kowane watan Satumba dai, al’ummar yankin Catalonia na gudanar da bikin Diada ko kuma ranar ‘yanci’ domin tunawa da ranar da Sarkin Spain Boourbon Philip ya kwace iko da birnin Barcelona, a shekarar 1714, yakin da ya kawo karshen cin gashin kan yankin na Catalonia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.