Isa ga babban shafi
Spain

Catalonia na gudanar da gagarumin yajin aiki

Al’ummar Catalonia na Spain na gudanar da yajin aikin game-gari a wannan Talata, in da suka dakile manyan hanyoyin sufuri, lamarin da ya gurgunta harkar kasuwanci.

Al’ummar Catalonia na Spain na gudanar da yajin aikin game-gari
Al’ummar Catalonia na Spain na gudanar da yajin aikin game-gari GABRIEL BOUYS / AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan yankin Catalonia ya zargi jami’an ‘yan sandan Spain da yin amfani da karfi wajen murkushe mutanen da suka fito kada kuri’ar raba gardamar ballewar daga kasar.

Yajin aikin game-gari da yankin Catalonia ya bukaci gudanarwa ya gurgunta harkar sufuri da kasuwanci da kuma makarantu, yayin da gwamnatin Madrid ke ci gaba da shan matsin lamba daga kasashen duniya don ganin cewa ta warware rikcin siyasa mafi muni da kasar ta gani a ‘yan shekarun baya-bayan nan.

Tashar jiragen karkashin kasa a birnin Barcelona ta takaita ayyukanta, yayin da masu zanga-zangar suka dakile manyan hanyoyin a sassan Catalonia, lamarin da ya haifar da cinkoson ababawan hawa.

Kazalika kungiyoyin kwadago na Catalonia da ke goyon bayan ballewa daga Spain da kuma cibiyoyin ra’aya al’adun gargajiya duk sun goyi bayan wannan yajin aiki, a wani mataki na nuna adawa da murkushewar da suka ce, ‘yan sandan Spain sun yi wa jama’arsu a lokacin kada kuri’ar ta raba gardama, lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar mutane 90.

A bangare guda, shugabannin yankin na Catalonia sun bayyana cewa, kimanin kashi 90 cikin 100 na a’ummar yankin sun goyi bayan ballewa daga Spain, amma gwamnatin Madrid ta lashi takobin dakatar da yunkurin na Catalonia.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta damu da rikicin siyasar Spain, yayi da kungiyar kasahen Turai ta bukaci gwamnatin kasar da ta kauce wa sake amfani da karfi kan jama’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.