Isa ga babban shafi
Faransa - Algeria

Macron ya bayyana takaici kan takun sakar Faransa da Algeriya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana takaicin sa kan takun sakar da kasar ta samu da Algeriya wanda ya haifar da rikicin diflomasiya, inda yace yana girmama kasar sosai.

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron.
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron. Yves Herman Pool/AFP
Talla

Wani babban jami’in fadar sa da ya nemi a sakaye sunan sa yace Macron ya damu da kalaman da suak haifar da tsamin dangantakar a tsakanin kasashen biyu, domin yana girmama kasar da tarihin ta da kuma ‘yancin ta.

Rahotanni sun ce Macron yayi kokarin dinke barakar da aka samu wajen gayyatar shugaban Algeria Abdelaziz Tebboune domin shiga tattauanwar da za’ayi wajen taron taimakawa Libya a ranar juma’a mai zuwa.

A makon jiya shugaba Tebboune yace ba zai zama na farko wajen mika hannu domin dinke barakarar da aka samu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.