Isa ga babban shafi
EU - korona

EU na buƙatar mambobinta su gaggauta daukar matakan magance korona

Hukumar kula da lafiya ta Tarayyar Turai ta yi kira ga kasashe mambobin EU da su gaggauta bullo da sabbin matakan rage ko kuma magance matsalar annobar Covid -19 daga nan zuwa watannin Disamba ko Janairu.

Ma'aikatan kiwon lafiya dake aikin rigakafin annobar korona a kasar Girka, 26/10/21.
Ma'aikatan kiwon lafiya dake aikin rigakafin annobar korona a kasar Girka, 26/10/21. AP - Giannis Papanikos
Talla

Daraktan Cibiyar Kula da Cututtuka masu yaduwa ta Turai, Andrea Ammon, ya ba da shawarar dabbaka shirin allurar rigakafin Covid ga wadanda suka haura shekaru 18, tare da yin taka tsan-tsan ga lafiyar wanda suka haura shekaru arba’in da haihuwa.

Hukumar ta kuma bukaci kasashe da su kara yawan adadin allurar rigakafin cutar, musamman ma wadanda ba su da isasshen magani.

Kasa da kashi 70 na yawan al’ummar kasashen Turai ciki har da kasashen Norway, Lichtenstein da Iceland an yi musu cikakkiyar allurar rigakafi, sai dai duk da haka akwai babban gibin rigakafin cutar da ba za a iya cike shi cikin kankanin lokacia ba, wanda shine ummul aba’isin yaduwar cutar yanzu haka, a cewar EU.

Gargadin nata ya zo kwana guda bayan Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce sama da mutane 700,000 za su iya mutuwa daga nan zuwa watan Maris din 2022 a Turai da Tsakiyar Asiya, baya ga miliyan 1.5 da suka rigaya suka kamu da cutar. .

Kungiayar Tarayya Turai ta ce sabon rahoton da hukumomin lafiya suka fitar ya nuna cewa nau’in cutuka, musamman irin su Delta ka iya karuwa sosai a cikin watannin Disamba da Janairu, sai dai idan an yi amfani da matakan kiwon lafiya yadda ya kamata tare da inganta shirin rigakafin cutar sosai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.