Faransa - Coronavirus
Mutane fiye da dubu 50 sun kamu da Korona cikin kwana 1 a Faransa
Faransa ta sanar da samun karin adadin mutane fiye da dubu 50 da suka kamu da cutar Korona cikin sa'o'i 24.
Wallafawa ranar:
Talla
Alkaluman da ma’aikatar lafiyar kasar ta fitar a jiya Asabar sun nuna hauhawar masu kamuwa da Koronar, duk da yi wa miliyoyin ‘yan kasar allurar rigakafi.
A jiya Asabar din dai mutane dubu 51 da 624 aka gano sun kamu da cutar Korona a fasin Faransa cikin sa’o’i 24, adadin da ya zarce na dubu 41 da aka samu a makon da ya gabata.
Zuwa yanzu jumillar mutane dubu 119 da 457 annobar Korona ta kashe a Faransa, tun bayan barkewar cutar a kasar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu