Isa ga babban shafi

Rasha za ta rufe ofisoshin Human Rights da Amnesty International

Gwamnatin Rasha ta sanar da yanke shawarar rufe ofisoshin hukumomin kare hakkin dan adam na Human Rights Watch da Amnesty International da suke aiki a kasar.

Shugaban Rasha Vladimir Poutine.
Shugaban Rasha Vladimir Poutine. AP - Mikhail Klimentyev
Talla

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Human Rights Watch ta shafe shekaru 30 tana gudanar da ayyukanta a kasar Rasha, yayin da ita kuma Amnesty ke cikin kasar tun shekarar 1993.

Zuwa yanzu gwamnatin Rasha ta dakatar da ayyukan kungiyoyin fararen 15 na kasashen waje a cikin kasar saboda keta dokokinta da ta ce sun yi, kamar yadda ma'aikatar shari'ar Rashan ta sanar.

Sanarwar ta zo ne a ranar Juma’a, rana ta 44 a yakin da Rasha ta kaddamar kan Ukraine, wanda yayi sanadin  mutuwar dubban mutane, yayin da wasu sama da miliyan 11 suka tsere daga gidajensu ko kuma ma suka bar kasar tasu, lamarin da ya haifar da matsalar 'yan gudun hijira mafi muni a Turai tun bayan wadda aka gani a yakin duniya na biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.