Isa ga babban shafi

Girka na fuskantar yanayin zafi da bata gani ba cikin shekaru 50

Kasar Girka na fuskantar tsananin mafi mafi girma a tarihin kasar cikin sama da shekaru 50, yayin da yanayin zafi sama ya kai sama da maki 40 a ma'aunin Celsius.

'Yan kwanakwana na kokarin kashe gobarar daji a Girka, 17/07/23.
'Yan kwanakwana na kokarin kashe gobarar daji a Girka, 17/07/23. REUTERS - STELIOS MISINAS
Talla

An gudanar da aikin gaggawa a tsibirin Rhodes a ranar Asabar don kwashe sama da mutane 1,500 don tsira daga gobarar dajin da ta shafe kwanaki biyar.

Tuni Girka ta kwashe kwanaki 11 cikin yanayin zafi , yayin da cibiyar kula da yanayi ta kasar ta yi gargadin cewa yanayin zai dauki lokaci mai tsawo, lamarin da ya kasance mafi dadewa da kasar ta taba gani.

Gobarar daji

Tsananin zafi ya afkawa Kasar ne a daidai lokacin take fama da gobarar daji a bangarorin kasar da dama.

A halin da ake ciki hukumomin kasar Girka sun gargadi mutane da kada su kuskura su fita, muddun ba dole ba saboda zafin da ya kafa tarihi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.