Isa ga babban shafi
Wasanni

Super Eagles na ci gaba da shan kaye gabanin gasar cin kofin duniya

Super Eagles ta Najeriya ta sha kaye a hannun jamhuriyar Czech da ci 1 mai ban haushi a wasan sada zumuncin da ya gudana a filin wasa na Rannersdorf da ke kasar Austria gabanin tunkarar gasar cin kofin duniya da ake gab da farawa a Rasha.

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles.
Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya Super Eagles. Reuters/Peter Cziborra
Talla

Ko a asabar din data gabata ma, sai da Super Eagles din ta sha kaye a hannun Ingila da ci 2-1 a wasan da ya gudana a Filin wasa na Wembley da ke London.

Haka zalika ta sha kaye a wasanni biyu har gida da ta karbi bakoncin Jamhuriyyar Dimokradiyyar Congo da kuma wanda ta karbi kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid, amma dai duk da haka ‘yan kasar na ganin akwai kyakkyawan zaton tawagar ka iya yin abin azo a gani a gasar cin kofin duniyar ta bana.

Eagles din dai na rukunin D ne a jadawalin gasar ta cin kofin duniya inda kum za ta kara da kasashen Argentina, Croatia da kuma Iceland, kuma was anta na farko shi ne za ta kara da Croatia 16 ga watan nan wato nan da kwana 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.