An kawo karshen neman jirgin da ya bace dauke da Emiliano Sala
Jami’an ceto sun sanar da kawo karshen neman jirgin saman fasinjan da sabon dan wasan Cardiff City Emiliano Sala ke ciki, wanda ya bace, a lokacin da ya taso daga Nantes zuwa Ingila.
Wallafawa ranar:
Mai magana da yawun tawagar jami’an ceton kaftin David Baker, ya ce sun gudanar da binciken da ya shafe murabba’in kilo mita dubu 1,700 akan teku, amma basu iya gano jirgin saman ko wata alamarsa ba.
Baker ya ce jiragen sama 3, tare da jirage masu saukar ungulu 5 ne suka shafe awanni 80 suna neman jirgin da yayi hadari, kafin kawo karshen aikin ceton.
A ranar Asabar da ta gabata, jirgin fasinjan da dan wasan gaba na Nantes Emiliano Sala ke ciki ya bace.
Dan wasan na kan hanyarsa ta zuwa Birtaniya don fara taka leda a Cardiff City.
Emiliano Sala mai shekaru 28 wanda Cardiff ta sayo daga Nantes ta Faransa kan euro miliyan 17, ya ci wa tsohuwar kungiyarsa ta Nantes kwallaye 13 a kakar wasa ta bana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu