Isa ga babban shafi
wasanni

Real Madrid ta casa Ajax a gidanta

Real Madrid ta doke Ajax a gidanta da ci 2-1 a fafatawar da suka yi a ranar Laraba a gasar cin kofin zakarun Turai.

Karim Benzema ya zura kwallo guda a karawar Real Madrid da Ajax a Amsterdam.
Karim Benzema ya zura kwallo guda a karawar Real Madrid da Ajax a Amsterdam. REUTERS/Wolfgang Rattay
Talla

Ajax dai ta doka tamaula yadda ya kamata a wasan, yayin da kuma aka soke kwallon da Nicolas Tagliafico ya jefa a ragar Madrid bayan nazarin fasahar hoton bidiyon da ke taimaka wa alakalin wasa yanke hukunci.

Fasahar ta nuna cewa, Tagliafico ya jefa kwallon ne bayan ya yi gaggawar wuce ‘yan wasan baya, wato abin da ake kira Offside a Turance.

A karon farko kenan da aka fara amfani da wannan fasahar ta bidiyo a gasar ta zakarun Turai, kuma ana iya cewa, ba ta yi wa Ajax dadi ba.

Shekaru 24 kenan raban da Ajax ta samu nasara akan Real Madrid mai rike da kambi.

Madrid ta zura kwallayenta ta hannun Karim Benzima da Marco Asensio.

Ita ma Tottenham ta lallasa Borussia Dortmund ta ci 3-0 a karawar da suka yi a Wembley, abin da ke nuna cewa, babu shakka ta kama hanyar samun gurbi a matakin Kwata Fainal a karon farko tun shekarar 2011.

Tottenham ta nuna bajinta musamman bayan dawowa daga hutun rabin lokaci, yayin da mai tsaren ragarta, Hugo Lloris ya kawar da kwallaye da dama.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.