Isa ga babban shafi
Austria

Austria ta kafa doka mai tsauri kan baki

Majalisar dokokin Austria ta amince da wata doka kan Bakin Haure daya kasance mafi tsauri a tarayyar Turai, tuni dai dokar ta fara shan suka daga Jam’iyyun adawar kasar da kungiyoyin kare hakkin dan adam.

Wasu 'yan gudun hijira a kan iyakar Austria
Wasu 'yan gudun hijira a kan iyakar Austria REUTERS/Leonhard Foeger
Talla

Dokar da ta samu shiga bayan samun yawan kuri’u 98 sama da 67 da ke adawa da shirin, za ta bai wa gwamantin kasar damar sanya dokar ta baci, idan aka samu karuwar bakin haure da kuma daina karban ‘yan gudun hijira da ke neman mafaka kai tsaye daga kan iyakokinta, cikin su har da na Syria da yaki ya raba su da kasarsu.

Jam’iyyun adawa da kungiyoyin kare hakkin dan adam sun soki dokar, da hukumar ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya ke gargadi cewa za ta cire rigar kariyar da Turai ke bai wa ‘yan gudun hijira.

Sai dai ministan cikin gidan kasar, Wolfgang Sobotka ya dage kan cewa Austria ba ta da zabi, tun da dai mambobin kungiyar kasashen Turai sun gaza taka taksu rawar wajen shawo kan kwararar bakin.

A cewar Sobotka, Austria ba za ta iya daukan illahirin nauyin bakin a kanta ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.