Isa ga babban shafi
Switzerland

An Bude Layin Dogo Na Karkashin Kasa Mafi Tsawo a Duniya

A kasar Switzerland,  yau Laraba aka kaddamar da layin dogo na karkashin kasa mafi tsawo a duniya mai suna Layin dogon Gotthard domin saukaka harkokin sufuri a kasashen dake tsakiyar Turai.

Shugaban Faransa  Francois Hollande da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Switzerland da Fira Ministan Italiya a tashan jirgin kasa na Gotthard.
Shugaban Faransa Francois Hollande da Shugaban Gwamnatin Jamus Angela Merkel da Shugaban Switzerland da Fira Ministan Italiya a tashan jirgin kasa na Gotthard. Reuters/路透社
Talla

Ganin yadda dorewar kungiyar kasashen Turai ke tangal-tangal, ga batun dimbin bakin haure dake tudada zuwa Turai, ga barazanar britaniya na ficewa daga kungiyar, Shugaban Switzerland Johan Schnelder-Amman, ya fadi a wajen kaddamar da layin dogon cewa zai taimakawa jama'a da tattalin arzikin Turai.

Bayan kammala jawabin nasa ne dai Jirgin farko ya zura kai tsawon kilomita 57, kuma cikin fasinjojin sa na farko sun hada da Shugaban Gwamnatin Jamus Uwargida Angela Merkel, da Shugaban Faransa Francois Hollande, da Shugaban Switzerland da kuma Fira Ministan  kasar Italia Matteo Renzi.

Samar da wannan layin dogo na karkashin kasa mai suna Layin dogon Gotthard dai kasar Switzerland ta dauki nayin samar dashi kuma an bi dashi ta kasashen na su.

Idan aka bude fara aiki da wannan layin  dogo  cikin watan 12 na wannan shekara, zai saukaka zirga-zirga cikin lokaci kadan tsakanin garuruwan Turai, da saukaka jigilan kayayyaki da kuma rage gurbacewar yanayi da motocin kan yi.

Shekaru 17 akayi ana aikin layin dogon, akan kudin Turai Euro biliyan 11 ko muce Dollan Amurka biliyan 12.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.