Isa ga babban shafi
Wasanni-Spain

Falcao da Coentrao na fuskantar shari'a

Lauyoyi a kasar Spain sun shigar da kara kan zargin da suke yi wa ‘yan wasan kwallon kafa da suka taka leda a kasar guda biyu, Radamel Falcao da kuma Fabio Coentrao, na boyewa ma’aikatar tattara harajin kasar, ainahin albashin da suke karba tsakanin shekarun 2012 da 2014.

Ana zargin Radamel Falcao da Fabio Coentrao, da laifin kin biyan haraji.
Ana zargin Radamel Falcao da Fabio Coentrao, da laifin kin biyan haraji. latribuna.hn
Talla

Jimillar kudaden harajin da lauoyoyin da ake zargin ‘yan wasan da kin biya ya kai euro miliyan 7.

Ana zargin Falcao, wanda a baya ya bugawa kungiyar Atletico Madrid a Spain, amma yanzu yake Monaco ta Faransa, da kin bayyana akalla euro miliyan 5 da dubu 600 da ya dafe a zamanin da yake taka leda a gasar Laliga.

Shi kuwa Fabio Centrao da ke kungiyar Real Madrid yanzu haka, an zarge shi ne da boye euro miliyan 1 da dubu 300 da ya karba a matsayin albashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.