Isa ga babban shafi
Wasanni

Dani Alves sakarai ne - Maradona

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona, ya bayyana Dani Alves dan kasar Brazil, da ke kungiyar Juventus, a matsayin Sakarai da bai san abinda yake ba.

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona.
Gwarzon dan wasan kwallon kafa na Argentina Diego Maradona. Reuters/Muhammad Hamed
Talla

Maradona ya bayyana haka ne cikin fushi, a lokacin da yake maida martani kan hirar da Alves yayi da wata kafar talabijin, inda Alves din ya ce bai kamata a rika kwatanta bajintar Maradona a fagen kwallon kafa da Lionel Messi ba.

A cewar Alves yin satar amfani da hannu wajen zurawa kasar Ingila kwallo da Maradona yayi, a wasan kusa dana karshe, na gasar cin kofin duniya, a shekarar 1986, ya isa abin kunya ga tsohon dan wasan, wanda kuma ‘yan baya bai kyautu su kwaikwaye shi ba, dan haka, bai kamata ma ya rika gama kansa da Messi ba, domin a cewarsa ko bada kwallo bai iya ba wato passing a turance.

Shi kuwa Maradona a martaninsa, cewa yayi Dani Alves, wanda ya bayyana a matsayin sakarai, cikin kowane rarraba kwallo 28 da yake yi, yayin da yake buga wasa, sau hudu kawai yake samu dai dai, wanda takwarorin da suka rike lambarsa a baya kamar su Cafu, da Maicon ba haka suke ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.