Isa ga babban shafi
wasanni

Chelsea za ta fitar da Barcelona a gasar zakarun Turai

Kocin Chelsea Antonio Conte ya yi amanna cewa, ‘yan wasansa za su fitar da Barcelona daga gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai a fafatawar da kungiyoyin za su sake yi a ranar 14 ga watan Maris a Camp Nou.

Kocin Chelsea Antonio Conte
Kocin Chelsea Antonio Conte Chelsea Twitter
Talla

Wannan na zuwa ne bayan kungiyoyin biyu sun tashi kunnen doki 1-1 a karawar da suka yi jiya a Stamford Bridge.

Dan wasan Chelsea Willian ya taka muhimmiyar rawa a fafatawar ta jiya, in da ya jefa kwallo guda a ragar Barcelona bayan ya kai hare-hare masu kyau har sau biyu amma hakarsa ba ta cimma ruwa.

Sai dai a minti na 75, Lionel Messi na Barcelona ya farke kwallon da Willian ya jefa a minti na 62.

A karon farko kenan da Messi ke jefa kwallo a ragar Chelsea a wasanni 9 da ya buga da ita, kuma Barcelona ta zarce Chelsea wajen rike kwallo amma ta gaza keta masu tsaren bayan Chelsea don zura kwallaye.

Ita kuwa Bayern Munich ta yi wa Besiktas dukan tsiya, in da zazzaga ma ta kwallaye 5-0 kuma Muller da Lewandowski dukkaninsu sun zura kwallaye biyu-biyu.

Sau 14 kenan a jere da Bayern Munich ke samun nasara a wasanninta, yayin da ta matukar gajiyar da Besiktas a wasan na jiya a gasar zakarun nahiyar Turai.

Kungiyoyin biyu za su sake haduwa zagaye na biyu a ranar 14 ga watan Maris a birnin Santanbul, wato gidan Besiktas a Turkiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.