Quadri ya lashe gasar kwallon tebur ta 'Nigeria Open'
Dan Najeriya, Aruna Quadri ya lashe kofin gasar kwallon tebur ta ‘Nigeria Open’ wadda ta gudana a filin wasa na Teslim Balogun dfa ke birnin Lagos.
Wallafawa ranar:
Quadri ya samu nasarar, bayan doke abokin karawarsa Antoine Hachard na Faransa da kwallaye 4-2.
Karo na farko kenan da dan Najeriyar ya lashe gasar, wadda hukumar kula da wasan kwallon tebur ta duniya ITTF ke shiryawa.
Dan Najeriyar wanda ke a matsayi na 18 a matakin kwarewa a fagen kwallon Tebur na duniya, ya samu kyautar dala dubu $5,000, sakamakon wannan nasara da ya samu.
A shekarar 2015, Aruna Quadri ya gaza lashe kofin gasar ta 'Nigeria Open', bayan shan kaye a hannun abokin hamayyarsa na kasar Masar, Omar Assar.
A bangaren mata kuma Guo Yan ‘yar kasar China ce ta lashe kofin kwallon tebur din, bayan lallasa takwararta Sun Chen da kwallaye 4-3.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu