rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Nijar

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Nijar za ta fara aikin shimfida bututun mai zuwa Chadi

media
Akwai yiwuwar shimfida bututun ka iya tallafawa tattalin arzikin kasar da ke fuskantar kalubale a yanzu. REUTERS/Enrique Castro-Mendivil

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta ce a karshen wannan shekara za ta gina bututun mai da zai dinga kai manta kasar Kamaru ta cikin Chadi domin fitar da shi kasuwannin duniya.


Ministan man kasar Fumakay Gado ya ce suna saran fara aikin kafin karshen wannan shekara.

Matukar dai aka kammala aikin shimfida bututun man, Jamhuriyar Nijar za ta dinga fitar da mai ganga 110,000 kowacce rana, sabanin ganga 20,000 da take fitar wa yanzu haka.