rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Najeriya BOKO HARAM

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Boko Haram sun kashe sojan Najeriya

media
Sojan Najeriya a arewacin kasar REUTERS/Warren Strobel

Mayakan boko Haram sun kashe akalla sojin Najeriya guda lokacin da suka yiwa tawagar dakarun kwantan bauna a kauyen Kamuya dake Jihar Barno dake arewacin kasar.


Wata majiyar soji ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, yan bindigar sun kai harin ne da misalin karfe 11.30 na rana, inda suka kashe soja guda da raunana wasu guda 3.

Kauyen Kamuya da mahaifiyar shugaban sojin Najeriya Janar Tukur Buratai ta fito, ya dade yana gamuwa da hare haren mayakan boko haram.

Gwamnatin Najeriya a dai-dai lokacin da kungiyar Boko Haram ke cika shekaru goma,hukumomin kasar na ci gaba da neman hanyoyin kawo karshen rikicin da ya lakume rayuka da dama a Najeriya dama wajen kasar.