rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Canada Lafiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Canada na shirin halatta tabar wiwi

media
Canada za ta ba mutanen kasar damar noma tabar wiwi a gida

Firaministan Canada ya gabatar da daftarin doka da ke halatta yin amfani da tabar wiwi a fadin kasar, inda Canada za ta kasance kasa ta biyu da ta amince a zuki tabar bayan Uruguay.


Justin Trudeau na fatan bai wa jama’a damar yin amfani da wiwi saboda dalilai na kiwon lafiya, duk da cewa akwai wata doka makamanciyar haka da aka kafa 2001 da ke takaita shan tabar.

Dokar da aka gabatar a jiya ta fi bai wa mabukata ‘yancin shan tabar ta wiwi a Canada wacce ake tunanin za tabbatar a 1 ga watan Yulin 2018 lokacin da ake hutu a kasar.

Gwamnatin Canada ta ce matakin zai taimaka wajen kula da yadda ake mu’amula da tabar a kasar.

Gwamnati ta kiyasta cewa daga 2018 mutanen Canada sama da miliyan hudu da rabi za su sha tabar wiwi ton 655 a shekara, inda kuma za su kashe kudi da ya kai sama da dala biliyan 4 na kudin kasar.

Dokar ta kunshi ba mutanben kasar ‘yancin noma tabar a gida domin amfaninsu.