Isa ga babban shafi
Venezuela

Rundunar Sojin Venezuela ta murkushe harin ta’addanci a kasar

Rundunar Sojin kasar Venezuela ta ce ta yi nasarar murkushe wani harin ta’addanci da aka kai barikin ta da ke birnin Valencia kuma yanzu haka tana farautar wasu daga cikin maharan.

'Yan tawaye Venezuela da suka bayyana kansu a fai-fan bidiyo
'Yan tawaye Venezuela da suka bayyana kansu a fai-fan bidiyo Reuters
Talla

Shugaba Nicolas Maduro ya ce wasu sojin haya 20 tare da wani sojin da ya gudu daga aiki suka kai hari sansanin, kuma tuni aka kashe 2 aka kuma kama 8.

Kamen ya biyo bayan wani fai-fan bidiyo da ke yawo a kafafan sada zumunta, yana bayyana yadda wata kungiyar maza sanye da kakin soji ke sanar da shirin kai hari kan gwamnatin Maduro, wanda ke shan soka daga kasashen duniya kan yadda ya ke tafiyar da Mulkin kasar.

Daruruwan mutane ne suka fantsama kan titunan birnin Valencia domin nuna goyon bayansu ga ‘yan tawayen, kazalika wasu shaidun sun bada rahotan samun harbe-harbe a cikin dare.

Sai dai anyi amfani da barkunon tsohuwa wajen tarwatsa masu zanga-zangar, a kokarin lafar da kura rikicin kasar mai dauke da akalla mutane miliyan 30.

Wannan al’amari a yanzu ya sake bayyana fushi da rashin zaman lafiya a kasar da aka shafe tsawon watanni 4 ana samun boren adawa da gwamnatin Maduro da aka bayyana a matsayin mai mulkin kama da karya, kazalika rashin kwanciyar hankalin na ci gaba da tasiri ga tattalin arzikin kasar.

Dakarun gwamnatin kasar sun fitar da sanarwa da ke tir da harin tare da nesanta kansu daga ‘yan tawayen da suka bayyana cewa na kokarin dagula tsaro a kasar da kuma jaddada biyayar su ga Shugaba Maduro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.