Isa ga babban shafi
Saudiya

An soma hajjin bana

Yau Laraba ake soma aikin Hajjin bana gadan-gadan a Saudi Arabia inda alhazzai sama da miliyan biyu za su bar garin Makkah zuwa Mina kafin su wuce zuwa Arfah, mafi muhimmaci ga aikin hajji.

Masallacin Haram a Makkah
Masallacin Haram a Makkah Reuters
Talla

Taron aikin Hajji shi ne taron mutane mafi girma a duniya duk shekara.

Janar Mansour al-Turki mai Magana da yawun ma’aikatar cikin gidan Saudiya ya ce an tsaurara matakan tsaro domin magance duk wata barazanar da ke iya tasowa, yayin da aka inganta harkokin sufurin da za su kwashi maniyatan daga Makkah zuwa Mina.

Alhazzan Iran na cikin mahajjatan bana bayan sun kauracewa aikin a bara sakamakon sabani tsakanin kasar da Saudiya.

A bana za a gudanar da aikin Hajjin ne cikin tsauraran matakai na tsaro saboda barazanar ta’addanci da kuma tashin hankalin da ake ci gaba da samu a kasashen Yankin Asiya.

Aikin Hajji yana cikin Shika Shikan Musulunci guda biyar da aka wajabta wa Musulmi ya gudanar akalla sau daya a rayuwar shi idan har yana da wadata kuma yana cikin koshin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.