Isa ga babban shafi
Najeriya

Kujerar Hajjin bana ta zarce Naira Miliyan daya da rabi a Najeriya

Hukumar kula da ayyukan hajji a Najeriya NAHCON ta fitar da farashin kujera da maniya a jihohi 21 na Najeriya za su biya hadi da birnin Tarayya Abuja. Sabon tsarin na bana ya sabawa na shekarun baya inda ake samun banbanci a farashin kujerar da maniyata ke biya a jihohin kasar.

Masallacin Kaaba a Makka Saudiya
Masallacin Kaaba a Makka Saudiya REUTERS/Ahmed Jadallah/File Photo
Talla

Kusan Karin kashi 50 aka kara na kudin kujerar hajjin ta bana.

Hukumar ta kuma kayyade kudaden gujuri akan dala 800. Sannan Mahajjata za su biya kudin hadaya Naira 38,000 ga hukumomin kula da aikin hajji na jihohi wadanda za su biya kudaden ga Bankin Jaiz.

A bana an kayyade wa maniyata farashin dala akan Naira 307, sabanin bara da maniyata suka samu sassauci akan Naira 197 duk da tsadar dalar a kasuwa.
Ana dai ganin tsadar dala a kasuwar canji a Najeriya ne ya haifar da karin kudin kujerar.

Kudin Kujera a Jihohi 21.

- Abuja: N1, 538,218.62

- Adamawa: N1, 530, 101,18

- Anambra: N1, 511,173,77

- Bauchi: N1, 523,122.41

- Benue: N1, 522,118.9

- Edo: N1, 551,331.87

- Ekiti: N1, 525,191.27

- Gombe: N1, 516,118.90

- Kaduna: N1, 535,503.68

- Kano: N1, 537,859.97

- Kebbi: N1, 534,659.85

- Kwara: N1, 501,571.27

- Nasarawa: N1, 544,894.16

- Niger: N1,525,483.30

- Ogun: N1, 561,943.97

- Osun: N1, 548,153.42

- Oyo: N1, 584,069.02.

- Plateau: N1, 529,036.80

- Sokoto: N1, 524,618.90

- Taraba: N1, 521,138.21

- Zamfara: N1, 510,461.65

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.