Isa ga babban shafi
Iran

Za mu mutunta yarjejeniyar nukiliyar Iran - EU

Kungiyar Tarayar Turai ta sha alwashin ganin ta cigaba da mutunta yarjejeniyar da aka kulla da kasar Iran game da batun aikin nukiliya duk da cewa Amurka na adawa da batun.

Ma'aikata a kusa da tashar samar da wuta ta amfani da nukiliya a Iran.
Ma'aikata a kusa da tashar samar da wuta ta amfani da nukiliya a Iran. REUTERS/Mehr News Agency/Majid Asgaripour/File Photo
Talla

A cewar jakadiyar Kungiyar Tarayar Turai Uwargida Federika Mogherini kungiyar za ta ga cewa an aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Ta fadi haka ne a wurin taron da ake yi a birnin Samarkand na kasar Uzbekistan cewa yarjejeniyar na da muhimmanci, domin ya nuna an sami nasara sosai ta fannin diplomasiyyar kasashen Turai da duniya baki daya.

A ranar 13 ga watan Oktoba ne dai Shugaban Amurka Donald Trump ya ki amincewa da yarjejeniyar da kasashen duniya suka kulla da Iran domin hana ta aikin nukiliya da mugun nufi da ake zargi tana yi.

Sai dai kuma wakilan majalisar Amurkan a wannan mako mai karewa sun fara nuna cewa kasarsu na na'am da yarjejeniyar da aka kullan da Iran na hana Iran aikin nukiliyan, sannan kuma ta sami sassauci gameda takunkumin da aka sa mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.