Isa ga babban shafi
Afghanistan

Harin kunar bakin wake ya hallaka mutane 48 a Kabul

Wani dan harin kunar bakin wake na kungiyar ISIS a kasar Afghanistan, ya kashe mutane 48 da suka hada da Mata da kananan yara lokaci guda, a yayin da ya jikkata wasu fiye da 100.

Wasu kenan da harin kunan bakin waye ya rutsa da su ke neman agaji a wani asibin birnin Kabul, Afghanistan, a yau Lahadi 22 ga watan Afurelu shekarar 2018
Wasu kenan da harin kunan bakin waye ya rutsa da su ke neman agaji a wani asibin birnin Kabul, Afghanistan, a yau Lahadi 22 ga watan Afurelu shekarar 2018 REUTERS/Mohammad Ismail
Talla

Harin dai ya faru ne a wajen wata cibiyar rajistar zabe da ke a birnin Kabul na kasar Afghanistan, kuma harin shi ne na farko-farko da aka kai domin dagula shirin yin zabe a kasar ta Afghanistan.

Wannan harin dai ya kara kawo kokanton da ake akan batun samar da tsaro ga al’ummar kasar a lokacin zaben ‘yan Majalisu da aka shata gudanarwa a ranar 20 ga Watan Okotoban bana, zaben da ake gani tamkar Zakaran gwajin dafi na zaben shugaban kasa da ke tafe a Badi.

An kai harin ne a Kofar shiga Cibiyar rajistar zaben kamar yadda shaidun gani da Ido su ka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP. Daukacin Ministocin Lafiya da na harkokin cikin gida sun tabbatar da aukuwar harin, kuma tuni  kungiyar IS ta dauki alhakin kai wannan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.