Isa ga babban shafi

Kasashen duniya na gaf da fadawa rikicin kasuwanci - Putin

Shugaban Rasha Vladimir Putin, ya yi gargadin cewa kasashen duniya na gaf da fadawa cikin gagarumin rikicin kasuwanci, sakamakon irin matakan da gwamnatin Amurka ke dauka domin bai wa masana’antunta fifiko.

Shugaban Rasha Vladmir Putin.
Shugaban Rasha Vladmir Putin. AFP Photo/Kirill KUDRYAVTSEV
Talla

Shugaba Putin ya yi gargadin ne a gefen taron tattalin arziki da ke gudana a birnin St Petersburg a ranar Juma’a, inda ya ce matakan da Amurka ke dauka na neman haddasa tarnaki ga sha’anin kasuwanci tsakanin kasashen duniya.

Putin, bai fito fili karara ya ambaci sunan shugaban Amurka Donald Trump ba a kalaman nasa, sai dai ya ce abin da duniya ke bukata a wannan zamani shi ne karfafa ma’amala da jama’a a maimakon sa-in-sa.

Shugaban na Rasha dai ya bayyana matakan da Amurka ke dauka a fagen kasuwanci da cewa sun yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, kafin daga bisani ya yi kakkausar suka a game da haraji da kuma takunkuman da Amurka ke sanya wa kamfanoni da kuma kasashen duniya a cikin ‘yan watannin baya bayan nan, ba tare da mutunta dokokin kasuwanci ba.

Akwai dai shugabannin kasashe da dama da ke halartar wannan taro na tattalin arziki a birnin St Petersburg, da suka hada Emmanuel Macron na Faransa da kuma Firaminista Shinzo Abe na Japan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.