rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya
Gaggauce
Kotun Kolin Najeriya ta tabbatar da nasarar Ganduje a matsayin gwamnan Kano

Brazil

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Sanda a Brazil na binciken wani tsohon jami'in Gwamnati

media
Jair Bolsonaro Shugaban kasar Brazil Fuente: AFP.

‘Yan Sanda a kasar Brazil na gudanar da bincike na kaddarorin tsohon Ministan waje na kasar Aloysio Nunes da ake zargi da hannu dumu-dumu cikin harkokin cin hanci da rashawa.


Tuni dai aka rutsa da ‘yan siyasa da dama a kasar ta Brazil, ana zargin da dama daga cikin yan siyasar Brazil da hannu a batutuwa da suka jibanci rashawa, lamarin da ya kai ga dakatar da tsohon Shugaban kasar Lula Da Silva da ya jima a tsare.

A lokacin yakin zaben kasar Shugaban kasar mai ci Jair Bolsonaro ya dau alkawalin yakar cin hanci da rashawa a kasar ta Brazil.

Samame da ‘yan sanda suka kai jihohi shida y aba su damar kama mutane da suka hada da Shugaban hadaddiyar kungiyar masana’antu na kasar Robson Andrade.