Isa ga babban shafi
Ecowas

ECOWAS na taron gaggawa kan Cote d‘IVoire

A yau Juma’a ne kasashen yammacin Africa ke gudanar da wani taron gaggawa a Abuja babban birnin Najeriya kan rikicin siyasar Cote d’Ivoire, inda Laurent Gbagbo ya tirje na kin amincewa ya sauka daga kujerar shugabancin kasar duk da kiran da kungiyar ECOWAS da Majalisar Dunkin Duniya suka yi masa. Wannan dai shi ne taro karo na biyu da Shugabannin na ECOWAS suka gudanar, kan tattauna rikicin siyasa da ya dabaibaye kasar bayan dakatar da kasar daga kungiyar sanadiyar Gbabo ya ki amincewa da bukatar ECOWAS na sauka daga karagar mulkin kasar bayan ya sha kaye daga abokin hamayyarsa Ouattara a zaben shugaban kasar da aka gudanar.Masu sharhi suna ganin taron na ECOWAS a yau kan iya cimma matsaya kan kakubawa kasar takunkumi na tafiye tafiye sanadiyar rikicin, kodayake har yanzu babu wata majiya da aka samu kan muhimman abubuwan da taron zai saka a gaba.Fadar Shugaba Sarkozy tuni ta bada sanarwar tattaunawar da Nicolas Sarkozy ya yi da takwaransa Shugaba goodluck Jonathan na Nijeriya, wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS a halin yanzu.Tuni dai Goodluck Jonathan ya aika wa Laurenta Gbagbo da wasika kan shugaban ya amince ya sauka daga mukamin shugaban kasar a madadin sauran kasashen kungiyar ta ECOWAS.  

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kuma shugaban kungiyar ECOWAS.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan kuma shugaban kungiyar ECOWAS. Reuters / Afolabi Sotunde
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.